ABNA24 : Kafin haka dai gwamnatin mamaya ta Isra’ila ta hana a shigo da alluran zirin na Gaza. Ya zuwa yanzu dai cutar korona ta kama mutane 53, 000 a yankin sannan 538 sun rasa rayukansu.
Fawzi Bargusi kakakin Hamsa ya ja kunnen Isra'ila kan hana shigowar alluran riga kafin cutar, samfurin Sputnik V ta kasar Rasha zuwa yankin. Ya kuma kara da yin hakan yana dai dai da take hakkin biladama sannan laifin yaki ne.
342/